Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona tayi kukan kura ta tumurmusa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sevilla a wasan zagaye na biyu na kusa da na ƙarshe na gasar Copa del Ray da ci 3 da nema.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona tayi kukan kura ta tumurmusa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sevilla a wasan zagaye na biyu na kusa da na ƙarshe na gasar Copa del Ray da ci 3 da nema.

Tun a wasan zagayen farko sai da Sevilla ta wanke Barcelona daci 2 da nema amma kuma hakan bai sa Sevilla sun kai wasan ƙarshe ba, bayan sunyi sakaci a daren jiya inda suka ga ta leƙo ta koma musamman a minti na 5 na ƙarshe.

Sai dai ana ganin tsautsayin rashin rabo ya hau kan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sevilla biyo bayan yadda suka sami bugun daga kai sai mai tsaron gida a mintina na 73 amma kuma suka zubar dashi.

Yanzu ta tabbata an fatattaki ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sevilla daga wannan gasa ta Copa del Ray biyo bayan yadda suka ga ta leƙo ta koma inda Barcelona ta sami damar kaiwa matakin wasan ƙarshe.

Check Also

Gwamantin Tarayya ta ce ba za ta tattauna da ’yan bindiga da ke addabar sassan kasar nan. Yayin jawabi ga Taron Tattaunawa kan Taron Kasa a Fadar Shugaban Kasa, Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, Janar Babagana Monguno (mai ritayi) ya yi fatali ta batun sulhu da ’yan bindiga. Fitaccen malamin Islama, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, wanda kuma tsohon hafsan soja ne na daga cikin masu ba da shawarar tattaunawar sulhu da ’yan bindigar domin a samu zama lafiya. Amma da yake bayani a Fadar Shugaban Kasa a jiya Laraba, Monguno ya ce yin sulhu zai sa ’yan bindigar su yi zaton cewa gwamanti ta gaza. Ya ce, “Gwamnati na kokarin shawo kan matsalar tsaro, kuma sun sha bayyana cewa akwai matakai biyu na magance ta –lallami, tattaunawa, da sauransu. Duk da cewa gwamnati ba ta adawa da tattaunawa da su, amma tsakanin da Allah dole gwamnati ta yi amfani da karfi a kan wadannan mutane saboda ba su da amana, tunda za’a yi magana da su amma su je su wani na daban kuma su ci gaba da cutar da al’umma

Gwamnatin Tarayya tace babu shulhu tsakanin ta da ’yan bindiga da ke addabar sassan kasar nan

Gwamantin Tarayya ta ce ba za ta tattauna da ’yan bindiga da ke addabar sassan …

error: Alert: Is not allowed !!!