Ƙungiyoyin Ƙwallon Ƙafan Dasukafi Jefa Ƙwallaye Abana

Akakar wasa ta bana a manyan gasar rukuni-rukuni ta ƙasashen turai guda biyar da ake dasu wato gasar Firimiyar Ingila da Laliga da Bundes Liga da Serea A da kuma gasar League 1 ta ƙasar Faransa.

Akwai jerin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan dasukafi yawan jefa ƙwallaye araga bayan kammala gasar tasu inda har yanzu ba a kammala gasar acan ƙasar Italiya ba yayin dayarage wasanni biyu a kammala gasar ta Serea A.

Ga jerin ƙungiyoyin tare da adadin ƙwallayen dasuka jefa da kuma adadin wasannin dasukabuga:

1. Manchester City, ta buga wasanni 38 agasar Firimiyar Ingila ta jefa ƙwallaye guda 102.

2. Bayern Munich, ta buga wasanni 36 agasar Bundes Liga inda ta jefa ƙwallaye guda 100.

3. Atalanta wadda take buga gasar Serea A inda ta buga wasanni 36 sannan ta jefa ƙwallaye guda 96 amma amwai ragowar wasanni guda 2 dazata fafata anan gaba.

4. Barcalona ta buga wasanni guda 38 inda tajefa ƙwallaye guda 86 agasar Laliga.

5. Liverpool ta buga wasannin gasar ajin Firimiyar Ingila guda 38 inda takefa ƙwallaye guda 85.

Check Also

Gwamantin Tarayya ta ce ba za ta tattauna da ’yan bindiga da ke addabar sassan kasar nan. Yayin jawabi ga Taron Tattaunawa kan Taron Kasa a Fadar Shugaban Kasa, Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, Janar Babagana Monguno (mai ritayi) ya yi fatali ta batun sulhu da ’yan bindiga. Fitaccen malamin Islama, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, wanda kuma tsohon hafsan soja ne na daga cikin masu ba da shawarar tattaunawar sulhu da ’yan bindigar domin a samu zama lafiya. Amma da yake bayani a Fadar Shugaban Kasa a jiya Laraba, Monguno ya ce yin sulhu zai sa ’yan bindigar su yi zaton cewa gwamanti ta gaza. Ya ce, “Gwamnati na kokarin shawo kan matsalar tsaro, kuma sun sha bayyana cewa akwai matakai biyu na magance ta –lallami, tattaunawa, da sauransu. Duk da cewa gwamnati ba ta adawa da tattaunawa da su, amma tsakanin da Allah dole gwamnati ta yi amfani da karfi a kan wadannan mutane saboda ba su da amana, tunda za’a yi magana da su amma su je su wani na daban kuma su ci gaba da cutar da al’umma

Gwamnatin Tarayya tace babu shulhu tsakanin ta da ’yan bindiga da ke addabar sassan kasar nan

Gwamantin Tarayya ta ce ba za ta tattauna da ’yan bindiga da ke addabar sassan …

error: Alert: Is not allowed !!!