ABU Zaria-Masu Garkuwa da Dalibai sun Bukaci Miliyan 270

Wadanda suka yi garkuwa da daliban jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Lahadi sun nemi kudin fansa da ya kai miliyan N270.

An kiyasce kudaden da masu garkuwan kenema daga hannun makusantan dalibai 9 da suka kama ya kai wannan adadin kudin, inda suka nemi miliyan 30 ga kowani dalibi a matsayin kudin fansar.

Guda daga cikin daliban da ya samu arcewa mai suna Dicson Oko, ya shaida wa manema labarai cewa masu garkuwar sun tuntubi iyalansa da cewar su bada naira miliyan talatin kudin fansar dan uwan nasu.

Oko, wanda ya gamu da raunin harbin bindiga a yayin farmakin da aka kai musu, ya ce duk da ya samu tsira daga ‘yan ta’addar amma yana cike da damuwar halin da abokan karatunsa suke ciki a hannun masu garkuwan.
Har ila yau wata ‘yar uwar daya daga cikin daliban da aka yi garkuwa da su, ta shaida cewar su ma masu garkuwar sun nemi miliyan 30 na kudin fansar dan uwansu da suka sace.

Daga bisani tace sun roki masu garkuwar da su tausaya su saki daliban domin basu da hali.

Check Also

Tattaunawa da Matashi Mai Dalilin Aure dan Shekaru 23

AR_ Gabatar mana da kanka da kuma aikace aikace da kake yi. Auwal_ sunana Auwal …

error: Alert: Is not allowed !!!