Addinin musulunci ya samu babban karuwa: Fastoci fiye da 42 da matayensu sun musulunta a Abuja

Addinin Musulunci ya samu babban karuwa na wasu fastoci 42 da Bishop biyu. Fastocin sun karbi musulunci ne tare da iyalansu a babban masallacin kasa da ke Abuja. An kuma gudanar da wani muhimmin taro domin wayar masu da kai a kan shika-shikan addinin Musulunci, Labari da muke samu sun nuna cewa wasu fastoci 42 da kuma manyan limaman bishop biyu tare da iyalansu sun amshi addinin musulunci.

An yi taron musuluntar da su ne a dakin taro na babban masallacin kasa da ke birnin tarayya Abuja. An kuma gudanar da taron kara ma juna sani na tsawon kwanaki bakwai domin wayar masu da kai a kan shika-shikan addinin Musulunci.

Twitter A wani wallafa da wata mai amfani da shafin Twitter, @AysherSadiq ta yi, an gano hotunan fastocin tare da iyalansu cikin shiga ta mutunci inda mazan suka sanya dogayen rigunan tazarce, matan kuma sun kasance sanye da hijabai. Aysher ta wallafa a shafin nata cewa: “Fastoci 42, bishops biyu da iyalansu sun amshi addinin Musulunci a dakin taro na babban masallacin kasa, Abuja. An gudanar da taron kwanaki bakwai domin koyar da su shika-shikan Musulunci.

Check Also

ABU Zaria-Masu Garkuwa da Dalibai sun Bukaci Miliyan 270

Wadanda suka yi garkuwa da daliban jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria a kan hanyar Kaduna …

error: Alert: Is not allowed !!!