AKIYAYI TASHIN HANKALI A RANAR ZABEN ASABAR MAI ZUWA–HUKUMOMIN TSARO A KANO

A dai dai lokacin da ya rage kasa da mako guda a gudanar da sabon zaben, a wasu kananun hukumomi guda tara anan kano, gamayyar Hukumomin tsaro anan kano da suka hadar da yansanda, Hukumar tsarop ta farin kaya wato DSS, sojoji, da sauransu, sunja kunnuwan yan siyasar dake wannan yanki da a kul suka yarda akayi tashin Hankali komai kankantarsa awannan yanki. Har ila yau kuma sun amunce a rubuce cewar, kowa zai gargadi yaransa da nufin a zauna lafiya.

Wannan kira ya fito ne ta bakin Kwamishinan yansandan Jihar kano Habu Sani Amadu inda yace hukumomin tsaro a kano ba zasu lamunci ko wanne irin tashin hankali ba daga yan siyasar, da watakila ka iya kaiwa da zub da jini a yayin zabukan da za`a gudanar a ranar Asabar mai zuwa.

Daga karshe dai yan takarkarun sun amunce a rubuce da shuwagabannin jam`iyyunsu cewar zasu tabbata anyi zabe lafiya an kuma gama lafiya ba tare da wani tashin Hankali ba.

Shugaban Hukumar tsaro na farin kaya alokacin da yake jawabinsa.

 

 

Check Also

WOMEN MUST BE RECOGNIZE AS ROLL MODELS NOT CARE GIVERS ONLY

In celebration of the 2019 International Women’s Day which comes up on 8th, March every …

error: Alert: Is not allowed !!!