Akwai Yiwuwar Gwamnati Tarayya ta Amince da Kudire kudiren ASUU

Gwamnatin tarayya kan iya amincewa da kowanne irin tsari amatsayin mafita kan kiki kakar dake tsakaninta da kungiyar ASUU akan tsarin biyan albashi na IPPIS.

Ma`aikatar kwadago da daukan Aiki ta kasa ce ta bayyana hakan ta bakin makwogwaronta Charles Akpan, yayin da yake ganawa da puanch, inda yace a shirya ma`aikatar take ta karbi kowanne irin tsari amma bisa sharradin bazata aminci da ma`aikatan Bogi ba.

Kuma dukkanin tsarin da zatai amfani dashi, sai ya kasance mai fatali da ma`aikatan Bogi da kuma dukkanin wata kuskunda ko almundahanar albashi.

Akpan yace cikin masu adawa da tsarin albashin bai daya na IPPIS sun karu, a jiya lahadi bayan kungiyar ASUU, akwai takwararta ta manyan malaman jami`o`i kasar nan, da kungiyar ma`aiakatan jami`o` NASU, da kuma kungiyar manyan ma`aikatan man fetir da iskar Gas, da Dukkaninsu sukace tsarin da ma`aikatan gwamnati dayace.

Idan za`a iya tunawa dai kungiyar ASUU ta tsunduma yajin aiki tun a ranar 23 ga watan maris sakamkon matsin lamba daga gwamnati cewa ma`aikatan kungiyar na cikin mutanen da za`a dora akan tsarin na IPPIS, da kuma sauran dalilai, inda ta gabatar da tsarin UTAS amatsayin tsarin da takeso a dorata amadadin Tsarin saboda kin amincewarta dashi.

Check Also

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo mai shekara …

error: Alert: Is not allowed !!!