You dont have javascript enabled! Please enable it!

AMFANI DA KARFIN SOJI KADAI BA ZAIYI MAGANIN TSARO BA – OBASONJO

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, ya ce jiran tsammanin Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wani abu sama da wanda yake yi a yanzu dai dai yake da jiran gawon shanu.
Olusegun Ya bayyana hakan ne jiya Litinin, yayin wani taro kan hanyoyin bunkasa tsaro da wata kungiya mai suna Global Peace Foundation and Vision Africa ta shirya a Abuja.
Tsohon Shugaban ya kuma ce amfani da karfin soja kadai ba zai kawo karshen matsalar ta’addanci ba, dole sai an hada da wasu dabarun.
Ya kuma ba da shawarar a kirkirar ’yan sandan jihohi, inda ya ce matsalar tsaro matsala ce da ta shafi yankuna, kuma kowane yanki shi ya fi sanin hanyoyin magance nasa.
Shi ma da yake nasa jawabin, Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a kasar nan Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na uku, kira ya yi ga shugabanni da su daina siyasantar da harkokin siyasa.

Check Also

Youtube zai fara karɓar haraji daga masu ɗora bidiyonsu a shafin

Shafin Youtube zai fara karɓar haraji daga masu ɗora fayafayen bidiyonsu a shafin

Kamfanin Youtube zai fara karɓar haraji daga masu ɗora bidiyonsu a shafin waɗanda ke zaune …

';
error: Alert: Is not allowed !!!