An bayyana ilimi a matsayin kashin bayan cigaban kowace al’umma.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin wani kunshi da jami’in shiyyar karamar hukumar birni Munzali Muhammad Hausawa ya fitar a yau, wanda yace bayanin ya fita ne ta bakin shugaban karamar hukumar birni Fa’izu Alfindiki, a yayin ziyarar gani da ido da ya kai zuwa sakatariyar ilimi ta karamar hukumar.

Alfindiki yace babu shakka zai bawa bangaren ilimi fifiko a karkashin mulkin sa, wajen tabbatar da ganin an samar da nagartacce kuma ingantaccen ilimin.

Anata bangaren sakatariyar ilimin karamar hukumar mai barin gado Bilkisu Shafi’u Muhammad, cewa tayi tsofaffin daliban firamaren karamar hukumar sun taka muhimmiyar rawa wajen gyaran makarantun firamaren Shahuci da Kwalli da gidan Makama da kuma Kurmawa, inda tayi kira ga shugaban karamar hukumar da ya samarwa sakatariyar ilimin sabon waje, duba da cewa wadda ake ciki yanzu tayi kankanta.

Daraktan mulki na karamar hukumar Auwalu Yarima Madobi, taya sakatariyar ilimin mai barin gado murna yayi, bisa yadda ta bawa harkar ilimi gagarumar gudunmawa.

Check Also

Gwamantin Tarayya ta ce ba za ta tattauna da ’yan bindiga da ke addabar sassan kasar nan. Yayin jawabi ga Taron Tattaunawa kan Taron Kasa a Fadar Shugaban Kasa, Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, Janar Babagana Monguno (mai ritayi) ya yi fatali ta batun sulhu da ’yan bindiga. Fitaccen malamin Islama, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, wanda kuma tsohon hafsan soja ne na daga cikin masu ba da shawarar tattaunawar sulhu da ’yan bindigar domin a samu zama lafiya. Amma da yake bayani a Fadar Shugaban Kasa a jiya Laraba, Monguno ya ce yin sulhu zai sa ’yan bindigar su yi zaton cewa gwamanti ta gaza. Ya ce, “Gwamnati na kokarin shawo kan matsalar tsaro, kuma sun sha bayyana cewa akwai matakai biyu na magance ta –lallami, tattaunawa, da sauransu. Duk da cewa gwamnati ba ta adawa da tattaunawa da su, amma tsakanin da Allah dole gwamnati ta yi amfani da karfi a kan wadannan mutane saboda ba su da amana, tunda za’a yi magana da su amma su je su wani na daban kuma su ci gaba da cutar da al’umma

Gwamnatin Tarayya tace babu shulhu tsakanin ta da ’yan bindiga da ke addabar sassan kasar nan

Gwamantin Tarayya ta ce ba za ta tattauna da ’yan bindiga da ke addabar sassan …

error: Alert: Is not allowed !!!