An fitar da jerin sunayen ‘yan wasa guda 8 da za su yi takarar lashe kyautar gwarzon ɗan wasan wata-wata a gasar ajin Premier ta ƙasar England.

An fitar da jerin sunayen ‘yan wasa guda 8 da za su yi takarar lashe kyautar gwarzon ɗan wasan wata-wata a gasar ajin Premier ta ƙasar England.

An fitar da sunayen ‘yan wasan da ga ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa daban-daban. Sai dai a wannan karon ma an sami sababbin fuska a wajen fitar da sunayen ‘yan wasan.

‘Yan wasan dai sun hadar da Jesse Linagard dan wasa Man United dake zaman aro a Westham United  da Joao Cancelo na Manchester City  sai Joachim Andersen na Fuham United da Harvey Barnes mai wasa a Leicester City da Bruno Fernandes na Manchester United sai Ilkay Gundogan na Manchester City da Ruben Neves dake taka leda a Wolverhampton Wanderers da kuma Raphinha na kungiyar kwallon kafa ta Leeds United.

Daga cikin wadannan ‘yan wasane dai za a zaɓi gwarzon dan wasa na watan Feburairu da ya gabata.

Tunidai shararren dan wasan Barcelona Leonel Messi ya lashen kyautar gwarzon dan wasan Laligar kasar sufaniya na watan fabarairun daya gabata.

Check Also

IMG Spraker Falgore

KNHA okays Governor Abba Kabir to appoints 25 Special Advisers

KNHA okays Governor Abba Kabir to appoints 25 Special Advisers The State House of Assembly …