An shiga kwana na 100 ana gudanar da zanga-zangar adawa da dokar da gwamnatin India

An shiga kwana na 100 ana gudanar da zanga-zangar adawa da dokar da gwamnatin India ta kirkiro ta kawo sauyi a harkokin noman kasar.

Wani dattijo mai suna Prem Singh mai shekara 65 ya kwashe kimanin wata biyu yana fita wannan zanga-zanga.

Ya baro kauyensu na Haryana da ke arewacin India a watan Disamba 2020, domin shiga zanga-zangar da dubban manoma a India suka shiga, a kan iyakokin kasar, kan bukatarsu ta sake bibiyar dokar da gwamnatin kasar ta kafa a watan Satumba kan noma.

Yayin da suke gangamin zanga-zanga a garin Singhu – da ke gefen Delhi – Prem ya ce yana kiran dansa Sanddep mai shekara 34 zuwa gida ko wacce safiya.

Check Also

IMG Spraker Falgore

Capacity building ; a morale booster for effective service delivery.. Speaker Falgore.

From the Legislative House, Kano State House of Assembly. Capacity building ; a morale booster …