An tabbatarwa da Tsohon Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi na II Halifancin Tijjaniyya a Nigeria

Dariqar Tijjaniyya Karkashin Jagorancin Halifa Makki Cisse Halifan Shehu Ibrahim Inyass, ta nada Sarkin Kano Daya gabata wato Malam Muhammad Sanusi na II, Khalifancin Tijjaniyya a Nigeria Baki daya, da Yammacin Yau Juma’a a Garin Sokoto.

A Cikin Jawabinsa Khalifa Cisse, ya Bayyana cewar Makasudin Baiwa Mallam Muhammad Sanusi na II wannan Halifanci na Dariqar Tijjaniyya, shine duba da wanchan lokacin da Shehu Ibrahim Inyass ya Baiwa Sarkin Kano Sir. Muhammad Sanusi na I, wannan Halifanci tare da cewar akwai Halifofin Shehun a Duniya.

Shehu Cisse ya Kara da cewa Halifofin Shehu Ibrahim na nan a Duniya, Amma duk da haka Shehu Ibrahim yace Marigayi Sarki Sanusi na I Halifansa ne, saboda Haka Yauma ga Muhammad Sanusi tunda Dan Halifan ne don haka shima Halifan ne yanzu.

Tuni dai aka Dade ana zaton hakan ka iya Kasancewa ga Sabon Halifan duba da irin gudunmawar Daya Baiwa Dariqar a zamanin Mulkinsa, Wanda harta Kai Yana fitowa dukkan Ranar Juma’a don yin Wazifa, shiyasa Jama’a Musamman Tijjanawan sukaita Jiran wannan Lokaci, yanzu Haka dai za’a iya cewa Sarki Sanusi na II, ya cika dukkanin burikansa na Gadon Kakansa wato Sarkin Kano Muhammad Sanusi na I, Kasancewar dukkanin wadansu Ayyuka na Alkhairi da Kakansa yayi Shima Halifan ya gajesu tsaf.

An tabbatar da wannan Halifanci ne, a Yau Juma’a duka Cikin Shirye-shiryen gabatar da Maulidin Shehu Ibrahim Inyass na Kasa, da akesa ran gabatarwa a Gobe Asabar idan Allah ya kaimu.

Yanzu Haka dai Masoya daga ko Ina na nuna Farin cikinsu da wannan Halifanci na Tijjaniyya da Sarkin Kano na 14 a jerin Sarakunan Daular Fulani wato Muhammad Sanusi na II, ya samu tare da fatan Alkhairi gareshi a Matsayin Sabon Halifan Tijjaniyya a Najeriya

Check Also

Mohammed Adamu

Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu, ya bayyana wa babbar kotun tarayya da ke Abuja cewa doka ta ba shi damar ci gaba da kasancewa a ofis har zuwa 2023 ko 2024.

Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu, ya bayyana wa babbar kotun tarayya da ke Abuja …

error: Alert: Is not allowed !!!