An yi wa shari’ar Musulunci kwakwarima a UAE, an halasta shan giya da zaman dadiro

Kasar hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta yi wa shari’ar Musulunci kwakwarima. A yanzu an halasta shan giya da zaman dadiro sabanin yadda ake a baya a kasar. Hakan ya biyo bayan kokarin da kasar ke yi na habbaka tattalin arzikinta tare da jan hankulan masu zuwa yawon bude ido.

A kokarinta na bunkasa tattalin arzikin kasarta da zamantakewa, kasar hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta yi wa wasu dokokin shari’ar Musuluncin kasar gyaran fuska, inda a yanzu ta halasta shan giya da zaman dadiro.

Wannan kwaskwarima da kasar ta yi yana zuwa ne a daidai lokacin da ta ke ci gaba da daukar hankulan masu zuwa yawon bude ido musamman daga kasashen Yamma.

A ganin UAE hakan da ta yi zai habbaka tattalin arzikinta tare da nuna wa duniya cewa ita kasa ce mai sassaucin ra’ayi, karbar sauyi da kuma tafiya da zamani. Wannan yunkuri ya biyo bayan wata yarjejeniya mai cike da tarihi da kasar ta dauka domin dawo da hulda tsakanin UAE da kasar Isra’ila, wacce ita ma ake sa ran za ta kara yawan masu yawon bude ido da zuba hannun jari.

Hakazalika lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke shirin gudanar da gagarumin taro na World Expo. An shirya gudanar da babban taron wanda ake sanya ran zai kawo harkokin kasuwanci masu tarin yawa da kuma baki kimanin miliyan 25 cikin kasar, ne a watan Oktoba. Amma kuma sai aka samu tsaiko saboda annobar korona.

Kasar wacce ke samun kaso biyar na kudaden shigarta daga masu yawon bude ido ta samu tarnaki sakamakon dokar kulle na duniya da kuma hana jiragen sama jigila. Sabon sauyin ya soke hukuncin da aka tanadar wa masu shan giya, sayenta ko mallakarta ga ’yan shekara 21 zuwa sama.

Ko da yake ana samun giya kusan a dukkan mashaya da wuraren shakatawar biranen kasar, a baya mutane na bukatar lasisin gwamnati domin sayarwa, jigila ko kuma shanta. Sabuwar dokar za ta kyale Musulmai wadanda a baya aka haramta wa mallakar lasisin giya su iya shan giya ba tare da wani matsala ba.

Check Also

Tattaunawa da Matashi Mai Dalilin Aure dan Shekaru 23

AR_ Gabatar mana da kanka da kuma aikace aikace da kake yi. Auwal_ sunana Auwal …

error: Alert: Is not allowed !!!