An yiwa gwamnan jihar kano Allurar riga kafin cutar corona a bainar jama’a

Allurar rigakafin korona

A yammacin wannan rana an yiwa Gwamnan jihar kano Abdullahi Umar Ganduje alurar rigakafin cutar corona a asibitin kwararru na murtala Muhammad dake a jihar nan

wannan ya na kunshe ne ta cikin wata sanarwa mai dauke das a hannu babban sakataren yada labarai na jihar kano Abba Anwar, inda yace an yiwa Abdullahi allurar ne a gaban manyan jamian gwamnati, manbobin majalisar sarakuna hadi da manyan jami’an lafiya  na jihar nan wanda babban likitansa Dr Fakaradeen Yahaya Muhammad ya masa.

Allura dai wadda itace karon  farko a jihar kano tun bayan da aka kawo ta jihar nan

kwamishinan lafiya na jihar kano Dr  Aminu Ibrahim Tsanyawa  ya bayyana gwamnatin Abdullahi Ganduje a matsayin gwamnatin da zatabi duk tsarin daya kamata don kawo karshen cutar ta covid 19

daga bisani kwamishinan ya yabawa gwamnati gandujen bisa kokarin da take na ganin ta yaki cutar ta covid 19 a jihar  kano

Check Also

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo mai shekara …

error: Alert: Is not allowed !!!