Ana Cigaba da Zanga Zangar #EndSars a Arewacin Najeriya

Gangamin #EndSARS a Jos, jihar Filato, ya zama rikici bayan  da wasu suka karbe zanga-zangar da ake cikin lumana
– An tattaro cewa harkokin kasuwanci sun tsaya yayinda aka lalata motoci da shugana masu yawa
– Sai dai, an tura yan sanda yankin da abun ya faru domin dawo da zaman lafiya Wani zanga-zangar #EndSARS da ake gudanarwa a garin Jos, babbar birnin jihar Filato, ya kaure ya zama rikici, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito. A cewar rahoton, an samu tashin hankali a hanyar Ahmadu Bello Way da ke garin Jos yayinda masu zanga-zanga suka sanya shingaye a babban titin da ke sada mutum da cikin birnin a ranar Talata, 20 ga watan Oktoba. A kan haka, wasu matasa sun samu sabani da wadanda suka sanya shingen, wanda hakan ya haifar da tashin hankali. An farfasa motoci da yawa sannan aka kona wasu, an kuma lalata shaguna. An tattaro cewa an rufe harkoki a birnin domin hana ci gaban barnar.

Check Also

Right Honourable Cidari 1

KNHA pledged to support Community Promotion Council…. Speaker Chidari.

Kano State House of Assembly has reiterated its support to Kano Promotion Council on its …