Anyi kira ga gwamnati da ta rika taimakawa yan kasuwa da kuma sanya su a harkokin gwamnati…

Anyi kira ga gwamnati da ta rika taimakawa yan kasuwa da kuma sanya su a harkokin gwamnati, duba da irin gudunmawar da su ke bawa gwamnatin, ta fuskar haraji da daukar mutane aiki.

Kiran ya fito ne ta bakin shugaban kasuwar yan Katifa dake Ibrahim Taiwo, Alhaji Ubale Walawa, jim kadan bayan da aka bude wani katafaran shagon siyar da katifa, wanda akayi jiya da misalin karfe 2 na rana, a kan titin Ibrahim Taiwo kusa da gadar sama ta Obasajo.

Shugaban kamfanin Alhaji Sa’du Sallari, ya nuna farin cikin sa tare da godiya ga A… da ya nuna masa wannan rana ta bude wannan shago.

Guda daga cikin wadanda suka halarci bikin ya bayyana cewar bude irin wadannan shaguna zasu taimaka wajen rage zaman banza.

Daga cikin mahalarta taron bude shagon har da manya manyan yan kasuwa da masu wasan barkwanci irin su Baba Ari, Malam Kwaram da saura da dama.

Daga karshe shugaban kamfanin Alhaji Sa’idu Sallari yayi godiya tare da bangajiya ga dukkan wadanda suka samu damar halartar taron.

Check Also

IMG Spraker Falgore

Capacity building ; a morale booster for effective service delivery.. Speaker Falgore.

From the Legislative House, Kano State House of Assembly. Capacity building ; a morale booster …