Bikin Kammala Gasar Ajin Firimiyar Ingila Ayau

Za’a iya cewa ta faru ta ƙare anyiwa mai zane ɗaya sata agasar ajin Firimiyar Ingila wato kakar wasa ta 2019 zuwa 2020 da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa guda 20 suke fafatawa a tsakaninsu.

Domin kuwa awannan yammaci na Lahadi 26 ga watan Yuli za ayi bikin kammala gasar inda tuni ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool ta zamo zakara kuma anyi bikin bata kofin tun tsakiyar makon daya gabata.

Haka zalika ayau ɗin wasu zasu san matsayinsu atsaiwar jaddawalin gasar musamman masu kokawar wakiltar ƙasar Ingila agasar zakarun nahiyar turai da kuma gasar ajin ƙwararru ta nahiyar turai sannan dakuma masu kokawar komawa aji na biyu na gasar.

Ga jerin wasannin da ƙarshe daza a fafata ayammacin yau:

Liecester City da Manchester United.

Crystal Palace da Tottenham.

West Ham da Aston Villa

Chelsea da Wolves.

Manchester City da Norwich.

Arsenal da Watford.

Newcastle da Liverpool.

Everton da Bournemouth.

Burnley da Brighton.

Southampton da Sheffield United.

Yazuwa yanzu an fafata wasanni guda 370 agasar ta Firimiya inda anbuga cikon wasanni guda 10 zaizama anbuga wasanni guda 380 kenan.

Check Also

premier league

An fitar da jerin sunayen ‘yan wasa guda 8 da za su yi takarar lashe kyautar gwarzon ɗan wasan wata-wata a gasar ajin Premier ta ƙasar England.

An fitar da jerin sunayen ‘yan wasa guda 8 da za su yi takarar lashe …