Birtaniya ta sanar da shirinta na daukar nauyin dukkan gasar Zakarun Turai a karshen kakar wasa ta bana inji Firaminista Boris Johnson.

Birtaniya ta sanar da shirinta na daukar nauyin dukkan gasar Zakarun Turai a karshen kakar wasa ta bana inji Firaminista Boris Johnson.

West Ham na fatan dauke Tammy Abraham daga Chelsea a karshen wannan kakar wasan. Dan wasan gaban mai shekara 23 da wasu ‘yan wasa biyu, Edie Nketiah na Arsenal mai shekara 21 da Ivan Toney na Brentford mai shekara 24 ma na cikin ‘yan wasan da su ke fatan sayewa.

Dan wasan baya na Reading Omar Richards mai shekara 23 zai koma Bayern Munich na wa’adin shekara hudu a karshen wannan kakar wasan.

Dan wasan gaba na Arsenal da Faransa, Alexandre Lacazette mai shekara 29 ya kuwa barin kungiyar a karshen wannan kakar wasan.

Check Also

Gwamantin Tarayya ta ce ba za ta tattauna da ’yan bindiga da ke addabar sassan kasar nan. Yayin jawabi ga Taron Tattaunawa kan Taron Kasa a Fadar Shugaban Kasa, Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, Janar Babagana Monguno (mai ritayi) ya yi fatali ta batun sulhu da ’yan bindiga. Fitaccen malamin Islama, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, wanda kuma tsohon hafsan soja ne na daga cikin masu ba da shawarar tattaunawar sulhu da ’yan bindigar domin a samu zama lafiya. Amma da yake bayani a Fadar Shugaban Kasa a jiya Laraba, Monguno ya ce yin sulhu zai sa ’yan bindigar su yi zaton cewa gwamanti ta gaza. Ya ce, “Gwamnati na kokarin shawo kan matsalar tsaro, kuma sun sha bayyana cewa akwai matakai biyu na magance ta –lallami, tattaunawa, da sauransu. Duk da cewa gwamnati ba ta adawa da tattaunawa da su, amma tsakanin da Allah dole gwamnati ta yi amfani da karfi a kan wadannan mutane saboda ba su da amana, tunda za’a yi magana da su amma su je su wani na daban kuma su ci gaba da cutar da al’umma

Gwamnatin Tarayya tace babu shulhu tsakanin ta da ’yan bindiga da ke addabar sassan kasar nan

Gwamantin Tarayya ta ce ba za ta tattauna da ’yan bindiga da ke addabar sassan …

error: Alert: Is not allowed !!!