A yau Alhamis ne ake sa ran Kungiyar Gwamnonin kasarnan NGF ta yi shirin aiwatar da wata ganawa ta musamman kan batun allurar rigakafin cutar Korona, inda za a yi ganawar ta hanyar bidiyo. Bayanin hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da kungiyar ta raba wa manema labarai …
Read More »Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta amince da hukuncin kisa ga masu fyaɗe
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta amince da hukuncin kisa da kuma ɗaurin rai-da-rai ga waɗanda aka kama da aikata fyaɗe. Dokar ta tanadi ɗaurin rai-da-rai ga wanda ya aikata laifin fyaɗe da kuma hukuncin kisa idan mutum ya saka wa wanda ya yi wa fyaɗen cuta mai karya garkuwar jiki …
Read More »Gwamnan jihar Bauchi ya ce yan Nigeria ba su bukatar neman izinin zama a ko wanne yankin kasarnan.
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya ce yan Nigeria ba su bukatar izinin wani gwamna kafin su zauna a ko wanne yankin kasar. A cewar Mohammed, yan kasa ba su bukatar izinin takwararsa na jihar Ondo, Rotimi Akeredolu kafin su zauna a dazukan da ke jihar ta Kudu ta …
Read More »Hukumar ICPC, ta zargi wasu ma’aikatu da hukumomi da aikata rashin gaskiya a kasafin kudin kasarnan.
Hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC, ta zargi wasu ma’aikatu da hukumomi da kuma cibiyoyi MDA da aikata rashin gaskiya, ta hanyar taba kasafin kudin kasarnan. Shugaban hukumar ICPC Farfesa Bolaji Owasanoye, ya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema Labarai, a babban birnin tarayya Abuja a …
Read More »Gwamnonin wasu jihohin Arewacin kasarnan sun kai ziyara a jihohin kudu maso yammacin kasar a kokarin wanzar da zaman lafiya
Gwamnonin wasu jihohin Arewacin kasarnan sun kai ziyara a jihohin kudu maso yammacin kasar a kokarin wanzar da zaman lafiya bayan fadan da ya barke a tsakanin Hausawa da Yarbawa a makon jiya. Gwamnonin sun hada da na Kano Abdullahi Umar Ganduje, da na Neja Abubakar Sani Bello, da kuma …
Read More »Shugaba Muhammadu Buhari ya nada sabon shugaban Hukumar dake yaki da yi wa tattalin arziki kasa ta’annati EFCC.
Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Abdulrasheed Bawa a matsayin sabon shugaban Hukumar dake yaki da yi wa tattalin arziki kasa ta’annati EFCC. Wata sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar Femi Adesina ya fitar a yau Talata ta ce, Bawa mai kimanin shekaru 40 a duniya, yana da kwarewa …
Read More »Shugaba Muhammadu Buhari yace gwamnatinsa za ta kare dukkan mabiya addinai da dukkan kabilun kasar nan
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace gwamnatinsa za ta kare dukkan mabiya addinai da dukkan kabilun kasar nan ko da kuwa suna da rinjaye a yankin da suke rayuwa ko kuma tsiraru ne su, kamar yadda tsarin mulkin kasa ya tanadar. Cikin wata sanarwa da Garba Shehu mashawarci ga shugaban kasa …
Read More »Covid – 19: An samu karin mutane 520 masu dauke da cutar corona a kasarnan
Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa a kasar nan NCDC ta ce an samu karin mutum 520 da suka kamu da annobar cutar Corona a kasar nan ranar Lahadi da ta gabata. La’akari da sabbin alkaluman da hukumar ta fitar, an rawaito jihar Ondo a matsayin ta farko cikin jerin jihohin …
Read More »Hukumar Tabbatar da Ingancin Kayayyaki ta SON ta Jinjinawa Kamfanin AMMASCO
Hukumar tabbatar da ingancin Kayayyaki ta Kasa wato (SON) tace za tayi duk mai yuwuwa wajen ganin ta bayarda dukkan wata kariya dake akwai wajen karfafa gwiwar Kamfanin Ammasco sakamakon Gamsuwa da yadda suke inganta Ayyukansu. Jawabin hakan ya fitone ta bakin Shugaban Hukumar Alh. Farouk A. Salim a wata …
Read More »Jami’ar East Carolina (ECU) ta musanta baiwa Ganduje mukamin Farfesa
Jami’ar East Carolina (ECU) dake kasar Amurka wacce a kwanaki aka rawaito na nada Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje a matsayin farfesa ta ce ba ta da masaniya a kan nadin. A cikin wata wasika da ta aikewa gwamnan, jami’ar ta ce sanarwar nadin wacce aka alakanta da daya …
Read More »