Ana ci gaba da ayyukan ceto a gaɓar teku ta Apam da ke kudancin Ghana inda wasu ƙananan yara 12 suka nutse yayin da suke ninkaya a wani wuri da aka hana shiga. Wata tawagar ƴan sandan kasar na aiki tuƙuru don gano gawarwakin yaran da yawansu ya kai 20. …
Read More »KASAR GHANA NA BIKIN CIKA SHEKARU 64 DA SAMUN YANCIN KAI.
Yau Asabar kasar Ghana ke bikin cika shekaru 64 da samun yancin kai daga turawan mulkin mallakar Ingila, sakamakon zaman kasar ta farko a Afirka da tayi watsi da mulkin mallaka a ranar 6 ga watan Maris na shekarar 1957. Kamar yadda aka saba yau an gudanar da shagulgula da faretin soji …
Read More »Fafaroma Francis ya soma rangadi irinsa na farko a Iraqi.
Fafaroma Francis ya soma rangadi irinsa na farko a Iraqi. Ya samu tarba daga manyan shugabanni a tashar jirgin sama Bagadaza, da faretin girmamawa, kade-kade domin yi masa marhaba. Wata majiya ta bayyana ziyarar a matsayin mafi hadari da shugaban darikar katolikar ke kaiwa kasashen ketare. Akwai damuwa kan yanayin …
Read More »Majalaisar Dinkin Duniya ta ce har yanzu tana dakon shaida da zai tabbatar da cewa Gimbiya Latifa ‘yar sarkin Dubai da aka kulle na raye.
Majalaisar Dinkin Duniya ta ce har yanzu tana dakon shaida da zai tabbatar da cewa Gimbiya Latifa ‘yar sarkin Dubai da aka kulle na raye. Majalisar ta nemi shaida daga gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa, kakakinta Rupert Colville ya shaida wa manema labarai cewa har yanzu babu wani martani da suka …
Read More »Tsohon shugaban kasar Ghana kuma shugaban ‘yan hamayyar kasar John Mahama ya ce bai amince da hukuncin Kotun Ƙolin ƙasar ba
Tsohon shugaban kasar Ghana kuma shugaban ‘yan hamayyar kasar John Mahama ya ce bai amince da hukuncin Kotun Ƙolin ƙasar ba, wadda ta tabbatar da zaɓen shugaba Nana Akufo-Addo. A ranar Alhamis ne kotun kolin ta yi watsi da korafin da aka shigar gabanta na cewa an yi magudi a …
Read More »Kotun ƙolin ƙasar Ghana ta tabbatar da nasarar Nana Akufo-Addo a zaben shugaban kasar da aka yi a watan Disambar
Kotun ƙolin ƙasar Ghana ta tabbatar da nasarar Nana Akufo-Addo a zaben shugaban kasar da aka yi a watan Disambar da ya gabata, tare da yin watsi da zargin an yi maguɗi a zaben. Tsohon shugaban ƙasar kuma babban dan hamayya a zaben John Mahama ne ya shigar da koken …
Read More »Kotun kolin Chadi ta bai wa shugaba Idris Deby wanda ke jagorantar kasar sama da shekara 30 damar sake tsayawa takara a karo na shida…
Kotun kolin Chadi ta bai wa shugaba Idris Deby wanda ke jagorantar kasar sama da shekara 30 damar sake tsayawa takara a karo na shida, a zaben shugaban kasar da za a yi a ranar 11 ga watan Afrilu mai zuwa. Shugaban zai fafata da ‘yan takara tara wadanda kotun …
Read More »Tsohon Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya jaddada aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugaban ƙasa.
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya yi amfani da jawabin da ya yi karon farko tun bayan da ya sauka daga kan mulki wajen jaddada aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugaban ƙasa. Trump na fatan yin takarar shugaban ƙasar ne ƙarƙashin jam’iyyar Republican a shekarar 2024. Ya faɗa wa taron …
Read More »Asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF yace kashin farko na rigakafin cutar Corona ya isa kasar Ghana.
Asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF yace kashin farko na rigakafin cutar Corona ya isa kasar Ghana. Cikin wata sanarwa da asusun ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce wannan ba karamin abin tarihi ba ne ga kasar a yunkurin da take na yaki da wannan …
Read More »Gwamnatin kasar Oman ta haramta wa jiragen kasarnan sauka a kasar
Gwamnatin Oman ta haramta wa jiragen kasarnan da wasu kasashen Afrika sauka a kasarta na tsawon kwana 15 saboda takaita yaduwar cutar korona. Cikin kasashen 10 da aka haramta wa sauka a Oman, ƙasashe takwas na Afrika ne. Kasashen sun hada da Najeriya da Afrika ta Kudu da Sudan da …
Read More »