Cibiyar CITAD za ta Horas da Matasa 5000 kan Amfani da Kafafen Sadarawa

Cibiyar Sadarwa da Cigaban Alumma ta CITAD ta ce ta shirya fara bayar da horo ga matasa dubu biya (5000) kan kyakykywa amfani da kafafen sadarwa na yana gizo (internet) domin tabbatar da kyakykyawan shugabanci da yakar cin hanci da rashawa har tsawon shekaru uku.

Shugaban cibiyar ta CITAD Engineer Dr. Y.Z Yau ya bayana hakan a yau Litinin yayin kaddamar da shirin da gidan rediyon da cibiyar ta samar tare da tallafin Cibiyar MacArthur.

Dr. Yau yace zuwan kafafen zumunta ya kara samarwa da dumukuradiya wajen zama da kuma baiwa yan kasa damar furtar albarkacin bakinsu a shugabanci a kafafen sadarwa.

Shugaban cibiyar ya kara da ceewa kafafen sada zumunta sun zama muryar jamaa sai dai har yanzu basu fahimci yadda zasu yi amfani da kafafen ba wajen taimakawa kasar nan ta cigaba ba. Don haka cibiyar ta shirya horaswar ga matasa dubu biyar.

“Mun samar da wannan shirin ne kurum domin tabbatar da shugabnci na gari da yakar cin hanci da rashawa a Najeriya, ita kuma rediyon da muka samar a yanar gizo domin bayar da horaswa ga daliban aikin jarida domin su fara koyon aiki sannan su gwada abinda suka koya a makarantunsu” Yunusa Yau.

Taron ya samu halartar Farfesa Habu Fagge da Kwamishinan Sadarwa na Jahar Kano Comrd Muhammad Garba wanda Sakataren dindin na maaikatar Usman Bala Muhammad ya wakilta.

Check Also

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo mai shekara …

error: Alert: Is not allowed !!!