Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Juventus da Argentina wato Paulo Dybala mai shekara 27 na iya barin kungiyar

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Juventus da Argentina wato Paulo Dybala mai shekara 27 na iya barin kungiyar domin akwai batun sayar da shi a karshen kakar wasa ta bana.

Cikin kungiyoyin da ke da bukatar Dybala akwai Liverpool, Manchester United da kuma Tottenham.

Tottenham da Borussia Dortmund  na kan gaba wajen kokarin daukar dan wasa Dean Henderson daga, Manchester United.

Henderson shi ne mai tsaran gidan Manchester United yana da shekaru 23.

Chelsea na kara samun karfin gwiwar daukar dan wasa Erling Braut Haaland, dan wasan gaba na Norway mai shekara 20 daga Borussia Dortmund.

Check Also

Gwamantin Tarayya ta ce ba za ta tattauna da ’yan bindiga da ke addabar sassan kasar nan. Yayin jawabi ga Taron Tattaunawa kan Taron Kasa a Fadar Shugaban Kasa, Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, Janar Babagana Monguno (mai ritayi) ya yi fatali ta batun sulhu da ’yan bindiga. Fitaccen malamin Islama, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, wanda kuma tsohon hafsan soja ne na daga cikin masu ba da shawarar tattaunawar sulhu da ’yan bindigar domin a samu zama lafiya. Amma da yake bayani a Fadar Shugaban Kasa a jiya Laraba, Monguno ya ce yin sulhu zai sa ’yan bindigar su yi zaton cewa gwamanti ta gaza. Ya ce, “Gwamnati na kokarin shawo kan matsalar tsaro, kuma sun sha bayyana cewa akwai matakai biyu na magance ta –lallami, tattaunawa, da sauransu. Duk da cewa gwamnati ba ta adawa da tattaunawa da su, amma tsakanin da Allah dole gwamnati ta yi amfani da karfi a kan wadannan mutane saboda ba su da amana, tunda za’a yi magana da su amma su je su wani na daban kuma su ci gaba da cutar da al’umma

Gwamnatin Tarayya tace babu shulhu tsakanin ta da ’yan bindiga da ke addabar sassan kasar nan

Gwamantin Tarayya ta ce ba za ta tattauna da ’yan bindiga da ke addabar sassan …

error: Alert: Is not allowed !!!