Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce “ya kamata” Babban Bankin kasa (CBN) ya sake duba matsayinsa na haramta amfani da kuɗin intanet

Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce “ya kamata” Babban Bankin kasa (CBN) ya sake duba matsayinsa na haramta amfani da kuɗin intanet a ƙasar wato cryptocurrency.

A farkon watan Fabarairu ne CBN ya haramta amfani da kuɗaɗen bisa dalilai na tsaro, yana mai cewa “ana amfani da su ne wurin ɗaukar nauyin ta’addanci da kuma halasta kuɗin haramun.

A jiya Alhamis, masu amfani da shafukan zumunta a Najeriya suka harzuƙa sakamakon kalaman  gwamnan Bankin, Godwin Emefiele, ya yi cewa ba za su taɓa amicewa da kuɗin intanet ɗin ba.

Check Also

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo mai shekara …

error: Alert: Is not allowed !!!