Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce jam’iyyar APC, kawo yanzu, ta yi wa mambobi miliyan 2.5 rajista a aikin rajistar/sabunta rajista a jihar Kano.

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce jam’iyyar APC, kawo yanzu, ta yi wa mambobi miliyan 2.5 rajista a aikin rajistar/sabunta rajista a jihar Kano. Sakataren watsa labarai na gwamnan, Abba Anwar ne ya sanar da hakan a ranar Litinin a Kano, rahoton Premium Times.

Mr Anwar ya ce gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC karo na shida da aka yi a Kano.

Kwamishinan ƙananan hukumomi da sarautu na jihar, Murtala Gari ya ce takardun rajistar da hedkwatar jam’iyyar na ƙasa ta bawa jihar Kano ba su wadata ba don haka suna buƙatar ƙari.

Check Also

Gwamantin Tarayya ta ce ba za ta tattauna da ’yan bindiga da ke addabar sassan kasar nan. Yayin jawabi ga Taron Tattaunawa kan Taron Kasa a Fadar Shugaban Kasa, Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, Janar Babagana Monguno (mai ritayi) ya yi fatali ta batun sulhu da ’yan bindiga. Fitaccen malamin Islama, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, wanda kuma tsohon hafsan soja ne na daga cikin masu ba da shawarar tattaunawar sulhu da ’yan bindigar domin a samu zama lafiya. Amma da yake bayani a Fadar Shugaban Kasa a jiya Laraba, Monguno ya ce yin sulhu zai sa ’yan bindigar su yi zaton cewa gwamanti ta gaza. Ya ce, “Gwamnati na kokarin shawo kan matsalar tsaro, kuma sun sha bayyana cewa akwai matakai biyu na magance ta –lallami, tattaunawa, da sauransu. Duk da cewa gwamnati ba ta adawa da tattaunawa da su, amma tsakanin da Allah dole gwamnati ta yi amfani da karfi a kan wadannan mutane saboda ba su da amana, tunda za’a yi magana da su amma su je su wani na daban kuma su ci gaba da cutar da al’umma

Gwamnatin Tarayya tace babu shulhu tsakanin ta da ’yan bindiga da ke addabar sassan kasar nan

Gwamantin Tarayya ta ce ba za ta tattauna da ’yan bindiga da ke addabar sassan …

error: Alert: Is not allowed !!!