Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci wadanda suka tsinci kansu cikin iftila’i daba-daban a jihar Kano dasu hanzarta yin rijista…

Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci wadanda suka tsinci kansu cikin iftila’i daba-daban a jihar Kano dasu hanzarta yin rijista da hukumar tallafawa gajiyayayu ta jihar Kano domin cin gajiyar tallafin gwamnatin tarayya.

Gwamna Ganduje ya bayyana hakane a yammacin jiya yayin rabon kayayyakin tallafi ga yan asalin jihar Kano wadanda iftila’in rikice rikice ya raba da mahallansu a jihohin da suke zaune da sauran masu bukata ta musamman dake jihar Kano wanda aka gudanar a harabar gidan gwamnatin Kano.

Dr Abdullahi Ganduje yace gwamnatin jihar Kano a shekarar data gabata ta tallafawa wadanda suka samu Kansu cikin iftila’in ambaliyar ruwa su kimanin dubu 34, da wadanda gobara ta raba da mahallansu su dubu biyu, da manoma dubu 10, da fulanin da aka sacewa shanunsu da kuma wadanda iska ta yayewa gidajen yayin damunar bana

A jabinsa tunda fari, kwamishinan hukumar agazawa yan gudun hijira ta kasa Dr. Bashi Garba Lado yace tallafin yana daya daga cikin manyan kudurorin gwamnatin tarayya na  tallafawa gajiyayyu da kuma yan gudun hijira.

Dr Lado ya kara da cewa  hukumar tasa ta bibiyi yan asalin jihar Kano wadanda suka dawo gida sakamakon  iftila’in rikice rikicen daya shafesu a wasu jihohin, domin cin gajitar tallafin gwamnatin tarayya kamar dai yanda aka gudanar a sauran jihohin Katsina da Zamfara da kuma jihar Borno.

Yana mai karin hasken cewa nan gaba kadan gwamnatin tarayya zata fara aikin gina gidajen da zaa tsuganar da yan gudun hijirar dake zaune a jihar Kano

Wakilinmu na gidan gwamnatin Kano Usman Abdu Kofarmata ya ruwai cewa daga cikin wadanda suka afana da tallafinnsun hadar da yan gudun hijira,  da masu larurar makanta, da kuturta, da guragu, da wadanda iftila’in ambaliyar ruwa ya raba da mahallansu,  da sauran  wadanda suka samu kansu cikin iftila’oin daban daban.

Kayayyakin da aka rabar dai sun hadar da kayayyakin abinci dana kwanciya da sauran kayayyakin bukatun yau da kullum.

Check Also

IMG Spraker Falgore

Capacity building ; a morale booster for effective service delivery.. Speaker Falgore.

From the Legislative House, Kano State House of Assembly. Capacity building ; a morale booster …