Gwamnatin jihar Kano ta bada tabbacin fara gudanar da allurar rigakafin cutar covid-19 a jihar Kano nan da makwanni biyu masu zuwa

Gwamnatin jihar Kano ta bada tabbacin fara gudanar da allurar rigakafin cutar covid-19 a jihar Kano nan da makwanni biyu masu zuwa.

Shugaban kwamitin kwararru kan yaki da cutar covid-19 a jihar Kano Dr. Tijjani Hussaini shine ya tabbatar da hakan yayin taron wayar da kan jamaa kan matakan dakile yaduwar cutar covid-19 daya kuntsi dukkanin shugabannin hukumomin tsaro na jihar Kano da kwararru a fannin kiwan lafiya wanda aka gudanar a fadar gwamnatin Kano.

Dr. Tijjani Hussaini yace an kasafta tsarin gudanar da allurar rigakafin zuwa gida hudu inda zaa fara da rukuni farko daya kunshi jamian kiwan lafiya da jamian tsaro wanda kuma  ake fatan  kammalawa a cikin shekar badi idan Allah ya kaimu kafin dorawa zuwa kashi na biyu dana uku da kuma hudu.

Inda ake sara yiwa mutane har kimanin dubu dari da hamsin zuwa da sittin a karo na farko na fara gudanar da rigakafin.

Saidai yace zaa fara kaddamar da allurar riga kafin ne daga kan matakin gwamnan jihar  Kano da sauran manya murarraban gwamnati, kamar dai yanda aka gudanar a matakin gwamnatin  tarayya.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Usman Abdu Kofarmata ya ruwaito cewa , Gwamnan Abdullahi Umar Ganduje ya jaddada muhimmnci dake tattare da rigakafin tare bukatar Alumma dasu garzaya cibiyoyin da aka kebe domin yin rijistar rigakafin.

Yana mai nanata cewa ta hanyar yin hakan ne zaa iya cimma nasarar kauda cutar baki daya.

Check Also

Gwamantin Tarayya ta ce ba za ta tattauna da ’yan bindiga da ke addabar sassan kasar nan. Yayin jawabi ga Taron Tattaunawa kan Taron Kasa a Fadar Shugaban Kasa, Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, Janar Babagana Monguno (mai ritayi) ya yi fatali ta batun sulhu da ’yan bindiga. Fitaccen malamin Islama, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, wanda kuma tsohon hafsan soja ne na daga cikin masu ba da shawarar tattaunawar sulhu da ’yan bindigar domin a samu zama lafiya. Amma da yake bayani a Fadar Shugaban Kasa a jiya Laraba, Monguno ya ce yin sulhu zai sa ’yan bindigar su yi zaton cewa gwamanti ta gaza. Ya ce, “Gwamnati na kokarin shawo kan matsalar tsaro, kuma sun sha bayyana cewa akwai matakai biyu na magance ta –lallami, tattaunawa, da sauransu. Duk da cewa gwamnati ba ta adawa da tattaunawa da su, amma tsakanin da Allah dole gwamnati ta yi amfani da karfi a kan wadannan mutane saboda ba su da amana, tunda za’a yi magana da su amma su je su wani na daban kuma su ci gaba da cutar da al’umma

Gwamnatin Tarayya tace babu shulhu tsakanin ta da ’yan bindiga da ke addabar sassan kasar nan

Gwamantin Tarayya ta ce ba za ta tattauna da ’yan bindiga da ke addabar sassan …

error: Alert: Is not allowed !!!