Hanya Daya ce da Zaa Magance Matsalar Rashin Tsaro a Najeriya_ Bukola Saraki

Tsohon shugaban majalisar dattijai, Dr. Abubakar Bukola Saraki ya fitar da jerin shawarwari kan yadda yake ganin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai magance matsalar rashin tsaro a Ƙasarnan.

Bukola Saraki ya ce guda daga cikin hanyoyin da shugaba buhari zai yi amfani da su shi ne yin aiki da tsofaffin shugabannin kasarnan da tsofaffin hafsoshin soji.

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan ya bayar da wannan shawarar ne daidai lokacin da lamuran tsaro ke cigaba da tabarbarewa a kasarnan, musamman sace-sacen jama’a ciki har da jami’an ƴan sanda 12 da aka sace a kwanakin baya.

Check Also

Tattaunawa da Matashi Mai Dalilin Aure dan Shekaru 23

AR_ Gabatar mana da kanka da kuma aikace aikace da kake yi. Auwal_ sunana Auwal …

error: Alert: Is not allowed !!!