Hukumar KAROTA tace ba gudu ba ja da baya kan biyan harajin Naira 100 -100

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jahar Kano (KAROTA) tace ba gudu ba ja da baya kan biyan harajin N100-100 daga matuka baburan adaidaita sahu duk da cewa sun yi zanga-zanga. Hukumar tace bukatar biyan harajin ya biyo bayan yarjejeniyar da akayi tsakanin gwamnati da kungiyoyin matuka baburan adaidaita sahun na jaharan.

Da yake magana da manema labarai, jami’in hulda da jama’a na hukumar KAROTA, Nabulisi Abubakar Kofar Na’isa, ya bayyana mamakinsa akan zanga zangar matuka baburar adaidaita sahun dukda yarjejeniyar biyan haraji da akayi da kungiyoyinsu.

Shima anasa bangaren shugaban kungiyar matuka baburan adaidaita sahun ya bayyana cewa sun roki gwamnati da ta ke karbar harajin naira 100-100 kullum amadadin karbar na watanni 6 ko fiye a lokaci guda dubada yanayin da ake ciki.

Tun a ranar Larabar data gabata ne wasu daga cikin matuka baburan suka fito kan manyan titunan kano suna zanga zanga dan su janyo hankalin gwamnati da masu ruwa da tsaki akan dubunnan kudaden da sukace hukumar ta KAROTA na tilasta musu biya aduk sanda ta bushi iska.

Check Also

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo mai shekara …

error: Alert: Is not allowed !!!