Hukumar kula da abinci da kwayoyi ta ƙasa (NAFDAC) ta amince ayi wa yan kasar nan rigakafin Astrazeneca

Hukumar kula da abinci da kwayoyi ta ƙasa (NAFDAC) ta amince ayi wa yan kasar nan rigakafin Astrazeneca wanda aka tabbatar da isowar ta tun a ranar talata datar wuce kamar yadda hukumar lafiya ta ƙasa ta bayyana haka a shafinta na Twitter.

Tun ranar Talata da rigakafin ta iso, an baiwa hukumar NAFDAC wasu don tayi gwaje-gwajen ta don tabbatar da ingancin allurar.

Da sakamakon gwajin ne, hukumar lafiya ke da damar fara yi ma ƴan kasar nan allurar rigakafin wanda aka tsara za’a fara yima ma’aikatan lafiya a sashen duba mara lafiya dake asibitin ƙasa a Abuja.

Check Also

IMG Spraker Falgore

KNHA okays Governor Abba Kabir to appoints 25 Special Advisers

KNHA okays Governor Abba Kabir to appoints 25 Special Advisers The State House of Assembly …