Hukumar Kula da Sufurin Jiragen sama ta Faransa tayi korafi akan 5G

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen sama ta Faransa ta bayyana cewar hanyar sadarwar 5G na yi wa sufurin jiragen sama illa, inda ta bukaci fasinjoji da su rika  kashe wayoyin hannunsu a yayin tafiya a cikin jiragen.

Mai magana da yawun hukumar ya ce amfani da wayoyin salular da ke dauke da hanyar sadarwar 5G na shafar tafiyar jiragen sama lokacin da jiragen ke sararin samaniya.

Sanarwar ta yi gargadin cewar, tiririn da ke fitowa daga wayoyin na shafar ayyukan jiragen kuma haka na iya haifar da babbar matsala, saboda haka ya dace a kauce wa amfani da wayoyin a lokacin tafiye-tafiye a sararin samaniya.

Har yanzu ana ci gaba da cece-kuce kan illar da fasahar ta 5G ke da ita, inda ko a bara aka rika yayata cewa, fasahar ce ta haifar da annobar coronavirus, amma tuni masana kimiya suka musanta wannan ikirari.

Check Also

Allurar rigakafin korona

An yiwa gwamnan jihar kano Allurar riga kafin cutar corona a bainar jama’a

A yammacin wannan rana an yiwa Gwamnan jihar kano Abdullahi Umar Ganduje alurar rigakafin cutar …

error: Alert: Is not allowed !!!