Hukumar Tabbatar da Ingancin Kayayyaki ta SON ta Jinjinawa Kamfanin AMMASCO

Hukumar tabbatar da ingancin Kayayyaki ta Kasa wato (SON) tace za tayi duk mai yuwuwa wajen ganin ta bayarda dukkan wata kariya dake akwai wajen karfafa gwiwar Kamfanin Ammasco sakamakon Gamsuwa da yadda suke inganta Ayyukansu.

Jawabin hakan ya fitone ta bakin Shugaban Hukumar Alh. Farouk A. Salim a wata ziyarar gani da ido daya kawo masana’ntar dake Jahar nan a Safiyar Yau.

Da yake nasa Jawabin Shugaban Kamfanin Ammasco Alh. Mustapha Ado Ammasco yace zuwan wannan Hukuma ba karamar nasara bace a garesu, kuma Hukumar ta ganewa Idanuwanta irin Kayayyakin da suke aiki dasu wadanda aka Amince dasu ne Hukumance.

Wakilinmu Shamsudden Mustapha Danhaki ya ruwaito mana cewa Shugaban Kamfanin na Ammasco ya jadda Manufarsu ta kara Bunkasa Kayayyakin da suke samarwa, wanda a gefe Guda yace su na iya kokarinsu wajen kyautata rayuwar ma’aikatansu da kuma tallafawa al’umma dake Makwabtaka dasu.

Check Also

Jam’iyyar PDP ta Kalubalanci Ziyarar da APC ta kaiwa Goodluck Jonathan

Jam’iyyar adawa ta PDP ta ce ziyarar da wasu gwamnonin APC suka kai wa tsohon …

error: Alert: Is not allowed !!!