You dont have javascript enabled! Please enable it!

Hukuncin Kotu: Duk da ruɗani, Ganduje ya buƙaci ƴaƴan jam’iyyar APC da su kwantar da hankulansu

Hukuncin Kotu: Duk da shiga ruɗani, Ganduje yace ahalin APC a Kano su kwantar da hankalinsu

Gwamna Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya buƙaci ƴaƴan jam’iyyar APC a Kano su sha kuriminsu kuma su kwantar da hankali akan hukuncin da kotu tayi na tabbatarwa da Ahmadu Haruna Zago Shugabancin APC.

Cikin jawabin da ya rabawa manema labarai, Kwamishinan Yaɗa labarai na Kano Malam Muhammadu Garba, yace rikicin cikin gida na jami’ar da ake fama dashi zaizo ƙarshe bayan nazartar hukuncin kotu da sukeyi a yanzu.

Sannan Ganduje ya baiwa jami’an tsaro umarnin tabbatar da bin doka ga wadanda ke neman kawo rikici, ko neman kawo ruɗani a Jihar Kano.

Ganduje ya kuma yabawa mambobin jam’iyyar APC, masu ruwa da tsaki wajen yiwa tsarin jam’iyyar biyayya a kowanne mataki.

Check Also

Mataimakin Shugaban Ƙasa Prof Yemi Osinbajo ya faɗawa Shugaban Buhari ƙudurinsa na tsayawa takarar a 2023

Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ya bayyanawa Shugaba Muhammadu Buhari aniyarsa ta tsayawa takarar Shugabancin …

';
error: Alert: Is not allowed !!!