Jami’ar Oxford ta ce an yi kutse a ɗaya daga cikin ɗakunan gwajin da take bincike kan cutar korona.

Jami’ar Oxford ta ce an yi kutse a ɗaya daga cikin ɗakunan gwajin da take bincike kan cutar korona.

Wani mai bincike kan harkokin tsaro a Birtaniya, Alex Holden, ya ce masu kutsen sun riƙa magana da Harshen Portuguese, kuma da alama sun aikata hakan ne daga Kudancin Amurka.

Wani kakakin Jami’ar Oxford ya ce babu wasu bayanan sirri da aka yi wa kutse kuma hukumar leken asiri ta Birtaniya na kan bincike.

Masana sun ce an samu ƙaruwar leƙen asiri ta internet da ake yi wa masana kimiyyar samar da rigakafi da kamfanonin haɗa magunguna a lokacin wannan annoba ta korona.

Check Also

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo mai shekara …

error: Alert: Is not allowed !!!