Jam’iyyar PDP ta Kalubalanci Ziyarar da APC ta kaiwa Goodluck Jonathan

Jam’iyyar adawa ta PDP ta ce ziyarar da wasu gwamnonin APC suka kai wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ta nuna amincewarsu karara kan gazawar APC.

A ranar Asabar ne dai gwamnonin APC karkashin jagorancin shugaban rikon kwarya na jam’iyyar Mai Mala Buni, suka ziyarci Jonathan a gidansa dake Abuja.

Sai dai ziyarar ta bar baya da kura, inda wasu a PDP ke ganinta a matsayin wani yunkuri na janyo tsohon shugaban kasar zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

PDP a wani jawabi da ta fitar ta hannun Sakataren yada Labaranta na kasa Kola Ologbondiyan, ta ce ziyarar ba komai ba ce face nuna gazawar APC.

A martanin da jam’iyyar APC ta yi wa PDP cikin wani jawabi da mataimakin sakataren jam’iyyar ya fitar, ya ce PDP ta rude ne da ziyarar da gwamnonin su ka kai.

Ya kara da cewa APC a matsayin jam’iyya za ta ci gaba da mayar da hankali ne ga abubuwan da zasu kawo nasara da ci gaban kasar.

Check Also

Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da hukuncin kisan da Babbar Kotun ta yanke a kan Maryam Sanda

Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin kisa da Babbar Kotun Birnin …

error: Alert: Is not allowed !!!