Kano: Daliban JSS1 da SS1 sun koma Makaranta

daliban aji daya (JSS1) na karamar sakanda da babbar sakandare (SS1) suka koma makaranta a jihar Kano.
Kwamishinan Iliminjihar, Muhammad Sanusi Kiru, ya sanar da hakan a sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a na ma’aikatar Aliyu Yusuf fitar.

“Ya kamata daliban makarantun Firamare 1-6 su sake komawa gaba daya daga ranar Litinin, 16 ga Nuwamba, sabanin umarnin farko da aka sanya musu ranakun zuwa makaranta”, inji shi.
Ya yi kira ga iyayen da yaransu ke wadannan azuzuwan da su yi biyayya ta hanyar dawo da su a ranakun da aka sanya.

Daga nan sai kwamishinan ya umarci daraktoci da shugabannin makarantu da sauran masu ruwa da tsaki da su kasance cikin shiri don ci gaba da aikin.

Idan ba a manta ba, gwamnatin jihar ta umurci daliban JSS-1 da SS-1 da su kasance a gida na tsawon makonni biyar domin an kammala jarabawar masu kammala karama da babbar sakandare.

Check Also

IMG Spraker Falgore

Capacity building ; a morale booster for effective service delivery.. Speaker Falgore.

From the Legislative House, Kano State House of Assembly. Capacity building ; a morale booster …