Kotu ta aike da Naziru Sarkin Waka Gidan Gyaran Hali

Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta kama Naziru M. Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin Waka da maraicen Laraba.

Kamun nasa na zuwa ne sa’o’i kadan da gurfanar da shi a gaban wata kotun a Kano bisa zargin sakin wasu wakoki biyu ba tare da tantancewar hukumar ba.

Fitaccen Darakta a Masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood kuma dan uwa ga Sarkin Wakar, Aminu Saira shine ya tabbatar da kamun a shafinsa na Twitter.

Saira ya wallafa a shafin nasa cewa, “Ina mai alhinin sanar da ’yan uwa da abokan arziki cewa Hukumar Tace Fina-finai karkashi Gwamnatin Jihar Kano ta sake kama dan uwana Naziru M. Ahmad (Sarkin waka).
“A yanzu haka yana tsare.
Karin bayani na nan tafe.”

Aminiya ta gano cewa an gabatar da mawakin ne bisa zargin sakin wakokin Gidan Sarauta da Sai Hakuri a ranar 12 ga Satumbar bara.

Da yake yanke hukunci yayin zaman kotun ranar Laraba, Mai shara’a Aminu Gabari ya ba da belin wanda ake kara a kan Naira miliyan biyu.

Kazalika, daga cikin sharadin belin, alkalin ya nemi Naziru ya kawo wadanda za su tsaya masa da za su hada da ko mahaifinsa, ko dan uwansa ko Dagaci ko Hakimin ko wani Kwamadan Hisbah a daya daga cikin kananan hukomomi 44 na jihar.

Check Also

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo mai shekara …

error: Alert: Is not allowed !!!