Kotu ta sake tabbatarwa da Dan-zago Shugabancin APC a Kano
Babbar Kotun tarayya ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Hamza Muazu ta sake tabbatarwa ɓangaren Sanata Malam Ibrahim Shekarau nasarar zaɓukan mazaɓu da na Ƙananan Hukumomi.
A ranar 30 ga watan Nuwamba ne dai kotun ta tabbatar da zaɓen da ɓangaren Gwamnati tayi a matsayin ya taka doka da ƙa’idojin zaɓe
Yayin da yake hukuncin a ranar Juma’a, mai Shari’a ya kori ƙalubalen da APC tayi tsagin Abdullahi Umar Ganduje tayi, tare da cin tara Naira Miliyan ɗaya akan ɓata lokacin kotu da sukayi.
Kotun kuma tace ɓangaren Shekarau da suka gudanar da zaɓen mazaɓu da ƙananan hukumomi a matsayin halastattu.