Kungiyar Kwadago ta fice daga Ganawarta da Gwamnatin Tarayya

Shugabanin kungyar kwadago sun fice daga ganawar da suke da gwamnatin tarayya domin cimma matsaya kan batun tashin gwauron zabi da farashin man fetir da wutar lantarki keyi a kasar nan.

Taron wanda aka shirya don sake duba aiwatar da matsayar da aka cimma yayin taruka uku da sukayi a baya, wanda shima aka tashi baran baran mintuna goma da shigarsa a dakin taro na Banquet dake fadar gwamnatin tarayya, Ganawar da aka fara karfe 8 na yammaci, ta samu halartar shugabanin kungiyoyin kwadago na kasa.

Tun da fari dai Shugaban kungiyar TUC ya zargi gwamnati da rashin Tabbas, ganin dukk zaman da ake a baya babu wata tartibiyar matsaya da suka cimma ta cigaba, hakan ya sanya su ficewa cikin fushi tare da fara fidda tsammai daga gwamnatin tarayya cikin bukatar da suke.

Sai dai ministan kwadago Chris Ngige ya bada tabbacin warware matsalar, inda yace yayin taron kasuwancn da zai gudana zasu tattauna kan batun, tare da bukatar yan jaridu ficewa daga Dakin taron cikin fadin nan da wani dan lokaci gwamnatin zata fitar da sanarwar matsayar da aka cimma bayan ganawar.

Anata banagren kungiyar NLC tace ta fice daga ganawar ne saboda yadda ta fahimci gwamnati bata da niyar kawo karshen matsalolin hauhawar fashin wutar lantarkin da man fetir.

Check Also

Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da hukuncin kisan da Babbar Kotun ta yanke a kan Maryam Sanda

Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin kisa da Babbar Kotun Birnin …

error: Alert: Is not allowed !!!