Kwararrun jam’ai na musamman daga rundunar yan sandan jihar Delta sunyi arangama da masu garkuwa da mutane ne

Kwararrun jam’ai na musamman daga rundunar yan sandan jihar Delta sunyi batakashi da wasu da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne tare da hallaka biyu daga cikinsu a ranar Alhamis.

Jami’an sun kuma yi nasarar ceto wasu mutum 16 daga hannun masu garkuwan tare da samun bindiga kirar AK-47 guda daya da mota kirar Toyota Highlander.

Kamishinan yan sandan jihar Ali Mohammed Ari, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai ta wayar tarho.

Yace ragowar mambobin kungiyar sun tserea a yayin musayar wutar inda wasunsu suka samu muggan raunuka.

Check Also

IMG Spraker Falgore

Capacity building ; a morale booster for effective service delivery.. Speaker Falgore.

From the Legislative House, Kano State House of Assembly. Capacity building ; a morale booster …