Lukaku ya kafa tarihi a gasar Serea A

Dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan dan asalin kasar Belgium wato Lukaku ya kafa tarihi a gasar Serea A, kuma a wasan hamayya na birnin Milan tsakanin Inter Milan da A.C Milan.

Lukaku ya kafa wannan tarihi ne a jiya bayan da kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan ta lallasa A.C Milan da ci 3 da nema, inda Lautaro Martinez ya jefa kwallaye biyu, inda Lukaku ya jefa kwallo daya.

Tarihin da Lukaku ya kafa shine ya zamo dan wasan daya jefa kwallaye a wasanni hamayya na birnin Milan har guda 4 a jere, inda a kowanne wasa Lukaku ya jefa kwallo a zaren A.C Milan, kuma rabon da a kafa wannan tarihi tun a shekarar 1950.

Check Also

IMG Spraker Falgore

KNHA okays Governor Abba Kabir to appoints 25 Special Advisers

KNHA okays Governor Abba Kabir to appoints 25 Special Advisers The State House of Assembly …