Ma’aikatar muhalli ta jihar kano ta jinjinawa hukumar kare faruwar hadura ta kasa reshan jihar kano

Ma'aikatar muhalli ta nan jihar kano ta jinjinawa hukumar kare faruwar hadura ta kasa reshan jihar kanoMa’aikatar muhalli ta nan jihar kano ta jinjinawa hukumar kare faruwar hadura ta kasa reshan jihar kano, bisa yadda suka himmatu wajan tsaftace muhallin su a koda yaushe.

Kwamishinan ma’aikatar muhalli ta nan kano Dr. Kabiru Ibrahim Getso shine ya bayyana hakan a lokacin rangadin aikin tsaftar muhalli mai kula da tashoshin motoci, kasuwanni, wuraran cin abinci, ma’aikatu dakuma hukumomin gwamnati.

Dr. Getso yana mai bayyana cewar ko shakka babu hukumar ta ciri tuta a fanin tsaftar muhalli musamman a wuraran da aka ziyarta kamar makarantar Hygiene, dakuma hukumar dake kula da manyam makarantun sakandire. 

Ya kuma yi kira ga sauran wurare dasu yi koyi daga gare su domin a cewar tsaftar muhalli yana taimakawa wajan yakar annobar cutar covid 19.

Wakilin mu Ibrahim Aminu Riminkebe ya rawaito mana cewar kwamishinan ya bukaci al’umma dasu zauna a gobe asabar domin tsaftar muhalli su wanda yake farawa tun daga karfe 7 zuwa karfe 10 na safiya, yana mai bayyana cewar akwai kotun tafi da gidan ka da zata hukunta duk wanda ya karya dokar tsaftar muhalli

Check Also

IMG Spraker Falgore

Capacity building ; a morale booster for effective service delivery.. Speaker Falgore.

From the Legislative House, Kano State House of Assembly. Capacity building ; a morale booster …