Maciya amana sun baibaye Gwamnatin Buhari – Sanata Ndume

Sanata Ali Ndume mai wakiltar Mazaɓar Borno ta Kudu ya ce maciya amanar Shugaba Muhammadu Buhari sune suka fi yawa a cikin gwamnatinsa…

Da yake tattaunawa da kafar yada labarai ta Channels TV, sanatan ya ce duk da cewa Buhari ya yi bakin ƙoƙarinsa, akwai mutanen da ke yi wa gwamnatinsa zagon ƙasa…

Da aka tamnbaye shi ko maki nawa zai bai wa gwamnatin jam’iyyarsu ta APC bayan shafe shekara biyar a kan mulki, sai ya ce: “Magana ta gaskiya ba ya jin daɗin yadda gwamnatin ke tafiya domin akwai kura-kurai da dama a cikin gwamnatin…

Yace Babban abin baƙin ciki shi ne, akwai abubuwan da suke faruwa waɗanda bai zama dole sai su faru ba. Sau uku suna ƙoƙarin ɗaura shugaban ƙasa Buhari a kan mulki amma baayi nasara ba, amma daga baya anyi nasara a karo na uku amna lamura ba sayiwa al’ummar kasa dadi…

Yace Na san Buhari mutumin kirki ne da ke son cigaban talakawa. Sai dai ɓarayi ne suka mamaye gwamnatin, abin da ya sa suke cin amanar tsare-tsaren da yake so ya gudanar.” A cewar Sanata Ndume…

Check Also

Tattaunawa da Matashi Mai Dalilin Aure dan Shekaru 23

AR_ Gabatar mana da kanka da kuma aikace aikace da kake yi. Auwal_ sunana Auwal …

error: Alert: Is not allowed !!!