Mai Martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya bayyana cewa cikin shekara guda, ya samu nasarar gyara alakar dake tsakanin Masarautar da Gwamnatin Kano

Mai Martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Ya Bayyana Nasarorin Daya samu Cikin Shekara Guda Daya shafe kan karagar Sarauta kano.

Sarkin ya Bayyana haka ne jim kadan bayan Kammala Taron Addu’ar murnar zagayowar Shekarar sa guda, daya ce an takaita Bukuwa saboda Hutar da Mutane Baki Daya.

yayin zantawarsa da Manema Labarai a Fadarsa ya shaida cewar, Cikin Shekara Guda, ya samu Nasarar Gyara zamantakewa tsakanin Masarautar da Gwamnatin Kano.

da Kuma samun damar Ziyartar Sauran Masarautu na Kasar Nan kamar yadda ya Gada daga Magabata.

Wakilinmu na Masarautar Shamsudden Mustapha Danhaki ya ruwaito Mana cewar Sarkin ya sha Alwashin hada Kai da sauran Jami’an Gwamnatin don Bude wata Kafa da zata Samarwa Matasa Ayyukan yi a Fadin Jihar nan, ta Hanyar Basu damar Amfani da Sabbin Fannonin Ilimi da Kimiyya don cimma burinsu ta Fuskar Ilimi Kasuwanci da Kuma zamantakewar Rayuwa Baki Daya.

Check Also

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo mai shekara …

error: Alert: Is not allowed !!!