Mai Martaba Sarkin Kano ya bukaci gwamnatin Kano da samar da katafariyar makaranta ta zamani…

Mai martaba sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya bukaci gwamnatin jihar Kano da tayi kokari wajen samar da katafariyar makaranta ta zamani wadda za ta lura da harkokin karatun tsangaya a karkashin masarautar sa ta Kano.

Sarkin ya mika wannan bukata ne lokacin da ya karbi tawagar Kwamishinan ilimi na jihar Kano da daukacin ma’aikatan sa, a wata ziyara ta musamman da suka kai masa a fadar sa jiya Talata.

Aminu Ado Bayero yace ko kadan masarautar sa ba ta kin tsarin koyarwar karantarwar Alkur’ani a makarantun allo, amma yana da burin ganin an samar da sabon tsarin da za’a tallafi bangaren.

Jami’in yada labarai na ma’aikatar ilimi Aliyu Yusuf ya rawaito a nasa bangaren Kwamishinan ilimi Muhammad Sanusi Sa’id Kiru na shaidawa Sarkin cewa, sun halarci fadar ne da nufin yin gaisuwa tare da neman albarkar sa da kuma neman goyon baya da hadin kan sa wajen inganta tsarin bayar da ilimi kyauta kuma dole da gwamnatin jihar Kano ta fito dashi.

Daga karshe Kwamishinan ya yaba da irin gudunmawa da Sarkin ke bayarwa musamman a bangaren ilimi da sauran harkokin gwamnati, abinda yace yana fata hakan za ta cigaba da kasancewa har zuwa nan gaba.

Check Also

Gwamantin Tarayya ta ce ba za ta tattauna da ’yan bindiga da ke addabar sassan kasar nan. Yayin jawabi ga Taron Tattaunawa kan Taron Kasa a Fadar Shugaban Kasa, Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, Janar Babagana Monguno (mai ritayi) ya yi fatali ta batun sulhu da ’yan bindiga. Fitaccen malamin Islama, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, wanda kuma tsohon hafsan soja ne na daga cikin masu ba da shawarar tattaunawar sulhu da ’yan bindigar domin a samu zama lafiya. Amma da yake bayani a Fadar Shugaban Kasa a jiya Laraba, Monguno ya ce yin sulhu zai sa ’yan bindigar su yi zaton cewa gwamanti ta gaza. Ya ce, “Gwamnati na kokarin shawo kan matsalar tsaro, kuma sun sha bayyana cewa akwai matakai biyu na magance ta –lallami, tattaunawa, da sauransu. Duk da cewa gwamnati ba ta adawa da tattaunawa da su, amma tsakanin da Allah dole gwamnati ta yi amfani da karfi a kan wadannan mutane saboda ba su da amana, tunda za’a yi magana da su amma su je su wani na daban kuma su ci gaba da cutar da al’umma

Gwamnatin Tarayya tace babu shulhu tsakanin ta da ’yan bindiga da ke addabar sassan kasar nan

Gwamantin Tarayya ta ce ba za ta tattauna da ’yan bindiga da ke addabar sassan …

error: Alert: Is not allowed !!!