Mamayar Da Paris Saint Germain Tayi Akakar Wasa Guda 6

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Paris Saint Germain dake ƙasar Faransa ta mamaye kusan dukkanin kofunan ƙasar Faransa da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa sama da 30 suke fafata kama daga gasar League 1 da kuma sauran ƙananan kofunan.

Inda acikin kakar wasa guda shida data gabata itace ta lashe kusan dukkanin kofunan na ƙasar ta Faransa inda tayi kakagida ta hana wata ƙungiya ta lashe.

Ga abubuwan dayafaru kamar haka:

1. Akakar wasa ta 2014 zuwa 2015 ta lashe dukkanin kofunan ƙasar Faransa guda 4.

2. Akakar wasa ta 2015 zuwa 2016 ta lashe dukkanin kofunan ƙasar Faransa guda 4.

3. Akakar wasa ta 2016 zuwa 2017 ta lashe kofuna guda 3.

4. Akakar wasa ta 2017 zuwa 2018 ta lashe dukkanin kofunan ƙasar Faransa guda 4.

5. Akakar wasa ta 2018 zuwa 2019 ta lashe kofunan ƙasar Faransa guda 2.

6. Akakar wasa ta 2019 zuwa 2020 ta lashe dukkanin kofunan ƙasar Faransa guda 4 rigis wato kakar wasa ta bana da aka kammala kenan.

Ayanzu dai za a iya cewa acikin kakar wasa guda shida da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Paris Saint Germain ta fafata a ƙasar ta Faransa ta lashe kofuna sama da guda 20.

Check Also

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona tayi kukan kura ta tumurmusa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sevilla a wasan zagaye na biyu na kusa da na ƙarshe na gasar Copa del Ray da ci 3 da nema.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona tayi kukan kura ta tumurmusa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sevilla …

error: Alert: Is not allowed !!!