Naira Miliyan Ɗari aka bayar kuɗin fansar Alwan Ali Hassan
Ƴan bindiga sun saki babban manajan bankin Gona, BOA Alwan Ali-Hassan.
Majiya dake kusa da iyalan babban manajan Bankin Ayyukan Gona, Alwan Ali-Hassan ya sanar da dawowar sa gida daga hannun ƴan bindiga.
Daily Nigerian ta buga cewa ɗan uwan Ali-Hassan sun biya kuɗin fansa kafin a ka sake sa.
Ali Hassan na daga cikin waɗanda ƴan bindiga suka yi awon gaba a harin jirgin ƙasa da suka kai a cikin makon jiya.
Gwamnatin Kaduna ta ce mutum 8 ƴan bindigan suka kashe sannan da yawa daga cikin matafiyan sun ji rauni.
Sannan maharan sun sace wasu da dama daga cikin matafiyan.