Darajar Hannayen jari a Najeriya ta faɗi kasa warwas a ranar Litinin bayan alƙalumman da aka fitar sun nuna ƙasar Nan ta samu koma-bayan tattalin arziki.
Haka kuma darajar naira ta ƙara faɗuwa a kasuwar bayan fage sakamakon ƙarancin dala a kasuwar.
Najeriya ta sake faɗawa cikin matsalar tattalin arziki karo na biyu a cikin shekaru huɗu.
Kuma alkalumman da aka fitar sun dora laifin kan tasirin annonar korona da kuma faɗuwar farashin mai a kasuwar duniya.
Ana sayar da dala ɗaya kan naira 484 a kasuwar bayan fage a ranar litinin, a farashin gwamnati kuma 381