You dont have javascript enabled! Please enable it!

Orji Kalu ya buƙaci a ɗage babban taron jam’iyyar APC da za’a gudanar a watan Fabrairu

Orji Kalu ya buƙaci a ɗage babban taron jam’iyyar APC da za’a gudanar a watan Fabrairu

Bulaliyar majalisar dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu, ya buƙaci Kwamitin ruƙon jam’iyyar APC na ƙasa ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Mai Mala Buni da su duba yiwuwar ɗage gudanar da babban taron jam’iyyar sakamakon rikicin da ke addabar APC a wasu daga cikin jihohin wannan ƙasa.

A cikin wata takarda da ya aikewa kwamitin ruƙon jam’iyyar ya yabawa jam’iyyar kan kokarin da takeyi na hada kan ƴaƴanta da kuma karbar wasu mambobin jam’iyyun don ganin APC ta cigaba da jan zaren ta.

Jam’iyyar na fuskantar ƙalubale a jihohi da dama tun bayan zaɓukan mazaɓu, ƙananan hukumomi, da kuma na Jihohi.

Check Also

Mataimakin Shugaban Ƙasa Prof Yemi Osinbajo ya faɗawa Shugaban Buhari ƙudurinsa na tsayawa takarar a 2023

Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ya bayyanawa Shugaba Muhammadu Buhari aniyarsa ta tsayawa takarar Shugabancin …

';
error: Alert: Is not allowed !!!