Rahotanni daga jihar Katsina a arewacin Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wasu mata kimanin 30

Rahotanni daga jihar Katsina a arewacin Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wasu mata kimanin 30 daga wani kauye a kudancin jihar da tsakar daren jiya.

Hakan ya zo ne bayan da wasu bayanan kuma suka ce maharan sun sace wasu matan fiye da 20 daga wasu kauyukkan biyu a shekaran jiya ranar Lahadi.

Sai dai jami’an tsaro a jihar ba su tabbatar da faruwar lamuran ba kawo yanzu.

jihar katsina dai na cikin jihohin arewa maso yammacin kasar nan, wanda ke fama da matsanancin rashin tsaro, abinda ke haddasa rasa rayuka  da tarin dukiya.

Check Also

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo mai shekara …

error: Alert: Is not allowed !!!