SARKIN KANO ALH. AMINU ADO BAYERO YA GODEWA ALLAH BISA SAMUN SHUGABA MUHAMMAD BUHARI A KASAR NAN.

Ya kuma yaba masa kan kokarinsa na zabo Dr. Isah Ali Ibrahim Fantami tare da bashi Ministan Sadarwa.
Kasancewar sanin irin mahimmanci da yake dashi a wannan bangare tare da kuma kokarin da yake dashi wajen ganin ya ciyar da Kasar gaba ta fannoni da dama

Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero yayi wannan Jawabi ne yayin da yake karbar Bakuncin Shugaban Hukumar Kamfanonin Sadarwa ta Kasa wato NCC, Professor Umar Garba Danbatta da Safiyar yau Litinin Fadarsa dake Kofar Kudu.

Daga karshe Sarkin ya kara jaddada Godiyarsa ga Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari bisa yadda ta baiwa Dan asalin Jihar Kano wannan Mukami na Shugabancin Hukumar kula da Kamfanonin Sadarwar Kasar nan wato NCC.

Wakilinmu na Masarautar Kano Shamsudden Mustapha Danhaki ya ruwaito mana cewa Farfesa Danbatta na tare da masu ruwa da tsaki na Hukumar tare da sauran Manya-mayan Jami’an Hukumar.

Check Also

Tattaunawa da Matashi Mai Dalilin Aure dan Shekaru 23

AR_ Gabatar mana da kanka da kuma aikace aikace da kake yi. Auwal_ sunana Auwal …

error: Alert: Is not allowed !!!