You dont have javascript enabled! Please enable it!

Sarkin Kano Zai Auri Tsohuwar Budurwarsa

Sarkin Kano Zai Auri Tsohuwar Budurwarsa

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero yana shirin angwancewa da tsohuwar sahibarsa wadda ake kira da suna Hajiyayye dake garin Dorayi a Kano.

Sarkin wanda matarsa ɗaya da ƴaƴa hudu zai yi auren bayan tsahon lokaci yana zaune da mace ɗaya.

Jaridar Daily Nigerian tace majiyarta ta bayyana mata cewar tuni shiri yayi nisa don tattaunawa da waliyyan yarinyar don sanya lokacin auren.

Majiyar tace an sha ɗaga lokacin auren sakamakon an shirya gudanar dashi ba tare da shirya bukukuwa irin na al’ada idan za’a yi aure a gidan sarauta.

“Mai martaba Sarki ya daɗe tare da Hajiyayye tun kafin ya zama Sarki” a cewar majiyar.

An haifi Aminu Ado Bayero a shekarar 1961, kuma shine Sarkir Fulani na 15 da Gwamna Kano Ganduje ya naɗa shi a ranar 9 ga watan Mayu, 2020.

Check Also

Mataimakin Shugaban Ƙasa Prof Yemi Osinbajo ya faɗawa Shugaban Buhari ƙudurinsa na tsayawa takarar a 2023

Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ya bayyanawa Shugaba Muhammadu Buhari aniyarsa ta tsayawa takarar Shugabancin …

';
error: Alert: Is not allowed !!!